Mun yi wa Boko Haram kofar rago - Buhari

Image caption Shugaba Faure Gnassingbé da kuma Muhammadu Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari na Nigeria ya ce dakarun hadin gwiwa sun yi wa mayakan Boko Haram kofar rago.

A cewarsa, a yanzu ana samun nasarar yaki da kungiyar musamman saboda hadin kai da Nigeria ke samu daga wajen kasashen da ke yankin tafkin Chadi.

Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da takwaransa na Togo, Faure Gnassingbé ya kai masa ziyara a Abuja.

Shugaban na Nigeria ya kara da cewar sun gano inda matsalar take, amma dai ya amince a kan cewar akwai matukar wahala yaki ta fuskoki daban-daban.

Tun bayan da Buhari ya hau karagar mulkin Nigeria a watan Mayu, mayakan Boko Haram sun hallaka mutane kusan 1,000.

A yanzu haka dai akwai rundunar hadin gwiwa tsakanin Nigeria da Niger da Kamaru da Chadi da kuma Benin mai sojoji fiye da 8,000 da ke yaki da Boko Haram.