Ghana ta dakatar da Alkalai bakwai

Alkalin Alkalai
Image caption Alkalin Alkalai ta Ghana Geogina Theodore Wood

Gwamnatin Ghana ta dakatar da bakwai daga cikin Alkalan babbar Kotun kasar su 12 da ake zargi da laifin karbar cin hanci domin juya shari'a.

Wannan sanarwar ta fito ne daga babbar mai shari'a ta kasar

Wani dan-jarida mai bincike Anas Aremeyaw ne dai ya dauki hotunan bidiyon alkalan a lokacin da ake zargin suna karbar hancin.

Dan jaridan ya ce yana da faifan bidiyo na kusan sa'oi 500 a matsayin hujja na abin da alkalan suka aikata, wanda aka gabatar wa Alkalin Alkalan kasar.

Tun daga wancan lokacin aka kafa kwamitin bincike.

Kwamitin binciken yana ci gaba da binciken sauran alkalan da ake zargi.