Gwamnatin Plateau ta kai Jang gaban EFCC

Image caption Jonah Jang tsohon gwamnan jihar Plateau yanzu sanata ne a majalisar dattijai

Gwamnatin jihar Filato da ke Najeriya ta kai karar tsohon gwamnan jihar Jonah Jang gaban hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa, EFCC saboda batan kimanin N200bn a lokacin gwamnatinsa.

Gwamnan jihar Solomom Lalong na zargin tsohon gwamnan da mukarrabansa da yin sama-da-fadi da kudaden domin, cewar sa, bai ga ayyukan da aka yi da su ba.

Gwamnan ya bukaci hukumar ta EFCC da ta kwato dukiyar da ake zargin sun wawure, ta kuma ladabtar da su.

Daukar wannan mataki, a cewarsa, ya biyo bayan karewar wa'adin mako biyu da gwamnatin ta bai wa tsohon gwamnan da mukarrabansa na su dawo da kudin cikin girma da arziki amma hakan ya faskara.

A hirar su BBC, Mista Pam Ayuba, kakakin tsohuwar gwamnatin Jihar Filaton ya musanta zargin.

Ya ce a shirye suke su amsa kirar hukumar ta EFCC domin gwamnatinsu ta yi amfani da kudin ta hanyar da ta dace.