Kura ta mamaye Gabas ta Tsakiya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yadda guguwa ta yi barna a Gabas ta Tsakiya

Kura ta mamaye ma fi yawan yankunan Gabas ta Tsakiya sakamakon wata iska da ruwan sama da aka yi masu tsanani, wanda suka yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Wasu hotunan da tauraron dan adam ya dauka na nuna yadda wata kura fara da ba tai kama da yashi ba ta lullube wasu bangarori na kasashen Syria da Lebanon da Isra'ila da kuma Cyprus.

Daruruwan mutane sun yi ta fama da matsala ta wahalar jan numfashi, kuma jami'ai sun shawarci mutane da su yi kokari su kasance a cikin gidajensu.

'Yan gudun hijirar Syria da ke zaune a sansanonin sune al'amarin ya fi shafa.

Alamu na nuna cewa kurar ba za ta washe ba nan da kwana daya.