Ana kokarin sauya tunanin 'yan Boko Haram

Image caption Shugaban Kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau

Bayanai daga gidajen yari daban-daban a Najeriya sun nuna cewa hukumomi na can sun dukufa kan kokarin sauya tunanin mayakan kungiyar Boko Haram da ake tsare da su a ciki, a matsayin wata hanyar yakar ta'addanci da tsattsauran ra'ayi ta ruwan sanyi.

Ofishin mai bai wa shugaban kasar shawara kan tsaro ne ke gudanar da aikin sauya tunanin nasu, a karkashin wani sabon shiri na yaki da tsattsauran ra'ayi da aka fi sani da CVE, wato Countering Violent Extremism.

Cibiyar yaki da ta'addanci ta duniya, Global Counter-terrorism Forum ce take daukar nauyin gudanar da wannan shirin a kasashen da ke fuskantar barazanar ta'addanci a duniya.

Tawagar BBC da ta kai ziyara zuwa wani gidan yari da ake tsare da irin wadannan mutane ta tarar suna yin wasan kwallon kafa cikin raha da annashuwa.

Akwai kuma malamai da suke yi musu wa'azi domin ganin sun canza halayensu.