Makkah: Za a gudanar da bincike

Hakkin mallakar hoto EPA

Hukumomin Saudiya sun soma bincike akan ƙugiyar ɗaukar kaya da ta faɗo a kan masallaci mai tsarki na Harami a makka a inda mutane 107 suka halaka, sannan mutane 240 suka jikkata.

Hukumomin Kasar sun ce wata iska ce mai karfi ta kada kugiyar, kuma ta kai gudun kilomita tamanin da uku a sa'a guda.

Aikin fadada babban masallacin dai na gudana domin baiwa karin musulmi dama a lokacin da wannan lamarin ya auku

Hukumomin Saudiyya dai sun soma aikin fadada masallacin na harami ne zuwa karin murabba'in sikwaya mita 40,000 a shekarar da ta wuce don masallacin ya dauki masallata kimanin miliyan biyu da dubu dari biyu a lokaci guda.

Mutane kusan miliyan guda ne suka isa kasar ta Saudiyya, gabanin aikin hajjin bana, wanda za'a soma cikin makonni biyu