Mutane bakwai sun rasu a sansanin 'yan gudun hijira

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Har yanzu babu cikakken bayani a kan harin.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya ta ce mutane bakwai ne suka mutu sakamakon harin bam da aka kai a sansanin 'yan gudun hijra da ke Yola a jihar Adamawa.

Lamarin ya auku ne sansanin 'yan gudun hijira da ke Malkohi a cikin Yola.

Babban jami'in watsa labarai na hukumar, Sani Datti, ya ce mutane 20 kuma sun jikkata.

A cewar sa, an bai wa bakwai daga cikin wadanda suka jikkata magunguna, kana aka sallame su; yayin da mutane 13 -- cikin su har da jami'an hukumar guda hudu -- ke ci gaba da samun kulawa a asibitin Tarayya da ke Yola.

Daruruwan mutane ne ke zaune a sansanonin kula da 'yan gudun hijirar sakamakon aika-aikar da 'yan Boko Haram suka yi.

A baya dai kungiyar Boko Haram ta sha kai hare-hare a garin na Yola.