'Yan gudun hijira dubu 40 za su isa Jamus

Hakkin mallakar hoto Getty

Ma'aikatar tsaro ta Jamus tace sojoji kusan dubu-hudu ne ke cikin shiri, domin taimakawa 'yan gudun hijira kimanin dubu -arba'in da ake tsammanin zasu isa kasar a karshen wannan makon.

Ministan Tsaron kasar ya ce sojoji sun shirya tsaf domin baiwa 'yan gudun hijirar taimako na kayayyaki idan akwai bukata

Wakilin BBC ya ce Taimakon da sojojin zasu bayar sun hada da samar da motocin da za'a kwashe su, da taimaka musu wajen cike takaddun neman mafaka, da kuma nema musu matsuguni a cikin barikin sojoji

A yau Asabar ake tsammanin dubban masu goyan bayan 'yan gudun hijirar, zasu gudanar da jerin gwano, a wani gangami a birane da dama na nahiyar Turai.

Za kuma a gudanar da wani jerin gwanon domin nuna adawa da kwararowar 'yan gudun hijirar