Mutane fiye da 80 sun mutu a India

Image caption Wadanda suka jikkata a fashewar abu a India

'Yan sanda a Indiya sun ce mutane fiye da tamanin sun rasa rayukansu ya yin da wasu da dama suka jikkata bayan da wani abu ya fashe a wani gidan cin abinci a tsakiyar jihar Madhya Pradesh.

Gidan cin abincin wanda ke kusa da tashar motoci bas-bas ya cika da ma'aikata da kuma yara dalibai inda suke yin kalaci a wajen.

Wata majiya daga 'Yan sandan ta ce fashewar abin ya faru ne bayan da Cylinder gas ta yi bindiga nan take kuma wuta ta kama.

Jami'an agaji na amfani da hannayen su wajen lalubo wadanda suka tsira yayinda ake amfani da abubuwan da ake kwashe baraguzai.