Kungiyar ICRC ta bada gudunmawar motoci

Kwamitin ya bayar da tallafi ne domin a taimakawa wadanda suka shiga wani hali sakamkon tashe-tashen hankulan da ake fama da su a arewa maso gabashin Najeriya.

Tun farkon shekarar nan dai kwamitin na ICRC da hadin gwiwar kungiyar bayar da agaji ta red cross a Najeriya sun taimakawa wadanda suka rasa matsugunan su ko kuma suka yi gudun hijra har kimanin 360,000 a jihohin Adamawa da Borno da Yobe da kuma Gombe.

Daga cikin abubuwan da suka bayar da tallafin sun hadar da abinci da tufafi da magunguna da dai makamantansu.