Saudiyya ta haramta yanka rakuma bana

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana daukar cutar MERS ta hanyar rakuma

Saudi Arabiya ta haramta yanka rakuma a biranen Makkah da Madina a lokacin aikin hajjin bana, bayan da aka samu karuwar mace macen da ake samu daga kwayar cutar MERS.

Binciken farko da hukumar lafiya ta Duniya ta wallafa, ya nuna cewa ta'ammali da rakuma na kara hatsarin kamuwa da cutar.

Hukumomin Saudiyya sunce tumaki da shanu---da basa dauke da kwayar cutar---sune kadai za a bada damar shigar dasu biranen masu tsarki a bana.

Mutane fiye da dari - biyar ne suka mutu a Saudi Arabiya, tun lokacin da aka gano kwayar cutar MERS a kasar a shekarar 2012