Buhari zai kai ziyara Faransa

Hakkin mallakar hoto
Image caption Faransa ta sha alwashin hada gwiwa da Najeriya domin magance matsalolin tsaro.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai kai ziyarar kwanaki uku kasar Faransa ranar Litinin.

Sanarwar da mai bai wa shugaban kasar shawara na musamman a kan watsa labarai, Femi Adesina ya aikewa kafafen watsa labarai, ta ce shugaban zai gana da takwaransa na Faransa, Francois Hollande, kuma za su tattauna ne a kan yadda kasashen biyu za su hada gwiwa domin shawo kan matsalolin tsaro da inganta kasuwanci.

Kazalika, Shugaba Buhari zai gana da ministocin tsaro da kudi da tattalin da kasashen waje na kasar ta Faransa.

Haka kuma, zai gana da jakadun kasashen Afirka da ke Faransa da 'yan Najeriya da ke kasar.

Kasar ta Faransa dai ta sha alwashin hada gwiwa da Najeriya domin murkushe kungiyar Boko Haram, wadda ta addabi Najeriya da makwabtanta irin su Jamhuriyar Nijar da Kamaru da Chadi, kasashen da ke da alaka da kut-da-kut da Faransa.

Shugaba Buhari zai yi tafiyar ne tare da mai ba shi shawara a kan tsaro Manjo-Janar Babagana Monguno da Manyan Sakatarorin ma'aikatun tsaro da kudi da aikin gona da harkokin kasashen waje da masana'antu.