Ana taron gaggawa a kan 'yan gudun hijira

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption wasu daga cikin 'yan gudun hijirar Syria

Kungiyar hadin kan kasashen musulmai za ta gudanar da taron gaggawa ranar Lahadin nan a birnin Jidda na Saudi Arabiya domin tattauna matsalar 'yan gudun hijira daga kasar Syria.

Kimanin mutane miliyan hudu da rikicin Syria ya raba da muhallansu ne ke zama a Jordan da Turkiya da kuma Lebanon, wasu daga cikin kasashen kungiyar hadin kan kasashen musulman.

Sai dai ana samun karuwar suka game da irin gudunmuwar Saudiya da kuma wasu kasashen larabawa dake yankin Tekun Fasha ke badawa.

A ranar Juma'a ce mahukuntan ma'aikatar harkokin wajen Saudiya suka ce akwai kimanin 'yan gudun hijirar daga Syria miliyan biyu dake zaune a Saudiya, sai dai ana nuna shakku game da wannan adadi da mahukuntan suka bayar.

Ganin yadda kasashen Turai ke fafutukar shawo kan matsalar 'yan hijirar da ke kwarara nahiyar, ana ci gaba da samun matsin lambar kan kasashen larabawa masu arziki da su suma su bada tasu gudun muwar wajen warware matsalar.