Shugaba Buhari ya gana da Hollande

Image caption Shugaba Buhari da Francois Hollande na Faransa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da takwaransa na Faransa Francois Hollande a ranar Litinin a ziyarar kwanaki uku da Buhari yake yi a Faransa.

Shugabannin biyu sun tattauna batutuwan samar da tsaro a Najeriya da bunkasa huldar kasuwanci a tsakanin kasashen biyu.

Rahotannin sun ce shugabannin sun tattauna yadda kasashen biyu za su hada gwiwa domin cimma wadannan batutuwa.

Kasar ta Faransa dai ta sha alwashin hada gwiwa da Najeriya domin murkushe kungiyar Boko Haram, wadda ta addabi Najeriya da makwabtanta irin su Jamhuriyar Nijar da Kamaru da Chadi, kasashen da ke da alaka da kut-da-kut da Faransa.

Shugaba Buhari ya yi tafiyar ne tare da mai ba shi shawara a kan tsaro Manjo-Janar Babagana Monguno da Manyan Sakatarorin ma'aikatun tsaro da kudi da aikin gona da harkokin kasashen waje da masana'antu.