Sojin Masar sun kashe 'yan yawon bude-ido 12

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jami'an tsaron Masar

Mahukuntan Masar sun ce jami'an tsaron kasar sun kashe mutane 12 -- ciki har da wasu 'yan kasar Mexico masu yawon bude-ido -- bayan sun yi zaton cewa 'yan ta'adda ne.

Ma'aikatar harkokin cikin gida a Masar ta ce sojoji da 'yan sanda a kasar sun kaddamar da wani farmaki lokacin da motocin da ke dauke da masu yawon bude-ido suke wucewa ta wurin da aka hana bi a hamadar yammacin kasar.

Gwamnatin Mexico ta tabbatar da mutuwar 'yan kasar ta guda biyu, yayin da shugaban kasar Enrique Pena Nieto ya yi Allah wadai da kisan.

Mista Pena Nieto ya bukaci gwamnatin Masar ta gudanar da cikakken bincike a kan lamarin.

A ranar Lahadi, wata kungiyar 'yan bindiga da take alakanta kanta da kungiyar IS ta ce akwai mayakanta a hamadar da ke kusa da iyakar Libya.