Ana kalaman batanci kan 'yan cirani a Facebook

Dandalin Facebook
Image caption Dandalin Facebook

Mahukuntan shafin internet na Facebook a kasar Jamus sun ce za su kafa wata hukuma don shawo kan nuna kin jinin 'yan cirani a shafinsu.

Sun ce ana samun karuwar kalaman nuna wariya, da kin jinin baki, a dandalin na facebook a kasar Jamus, da ke faruwa a daidai lokacin da ake samun kwararar 'yan gudun hijira a kasar.

Bayan matsin lambar na hukumomin Jamus, dandalin na Facebook ya ce zai tsaurara matakan sa ido tare da cire duk wasu kalaman batanci cikin gaggagwa.