Cin hanci: Cif Jojin Ghana ta bara

Image caption Babbar mai shari'a ta Ghana, Justice Georgina Theodora Wood ta bara kan badakalar cin hanci a karon farko

Babbar mai shari'a ta Ghana ta yi magana a fili a karon farko, tun lokacin da aka yi wani abin kunyar cin hanci da ya shafi bangaren shari'a na kasar.

Georgina Theodora Wood ta yi alkawarin daukar kwakkwaran matakin gaggawa a kan alkalan manya da na kananan kotuna 34 da aka zarga da karbar cin hanci.

An dai mikawa babbar mai shari'ar wani faifan bidiyo mai tsawon sa'o'i kusan 500 na shaida, sakamakon wani bincike da wani dan jaridar kasar ya kwashe tsawon shekaru biyu yana yi.

Haka kuma an ce jami'an kotu 180 ne aka a cikin abun kunyar.