Za a rage ma'aikatan jirgi saboda kibarsu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An fi son ma'aikatan cikin jirgi sun kasance 'yan caras marasa kiba

Kamfanin jiragen sama na Indiya yana shirin rage ma'aikatan jirgi su kimanin 125, saboda a cewarsa sun yi kiba da yawa.

Wani jami'in jiragen sama na Indiya ya shaida wa BBC cewa an dauki matakin ne saboda bin dokar da hukumar zirga-zirgar jiragen sama ta bullo da ita wadda ta shafi nauyin jiki a bara.

Jami'in ya ce kamfanin jiragen saman ya gargadi ma'aikatansa kimanin 600 su rage kiba, amma har yanzu 125 daga cikinsu ba su rage kibar yadda ake bukata ba.

Ya ce an lura cewar ma'aikatan cikin jirgi masu kiba ba sa iya taimakawa yadda ya kamata a lokacin da wani al'amari da ke bukatar taimakon gaggawa ya faru.