Kamfanin Nintendo zai samu sabon shugaba

Image caption Wasan kwamfuta na Mario

Za a nada babban Daraktan kamfanin Nintendo da ya fi kowanne dadewa, Tatsumi Kimishima a matsayin shugaban kamfanin, saboda mutuwar Satoru Iwata a watan Yuli.

Mista Kimishima ya kasance babban Daraktan kamfanin ton a watan Yunin 2013, kuma a shekarar 2000 ya fara aiki da kamfanin.

Kamfanin ya ce yana yin nade naden mukamai ne a matsayin wani bangare na bunkasa tsarin tafiyar da kamfanin na Nintendo.

A ranar Laraba ne za a fara aiki sauye sauyen da kamfanin ya ke yi.

Shima Mista Shigeru Miyamoto wanda yake kirkiro wasannin kwamfuta na Nintendo, an bashi lambar yabo ta kirkire kirkire.

Kazalika shima Mista Genyo Takeda, wani babban jami'in kamfanin, an bashi lambar yabo ta Fasaha.

Kamfanin ya ce an bashi lambar yabon ne domin a nuna muhimmancin rawar daya taka wajen ba kamfanin shawarori.