Turai ta kasa cimma matsaya a kan 'yan ci-rani

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kasashen turai suna rufe iyakoki saboda 'yan gudun hijra

Taron da ministocin kasashen Tarayyar Turai suka yi a Brussels a kan shirin nan mai cike da takaddama na sake tsugunar da 'yan gudun hijra 620,000 ya watse ba tare da cimma matsaya ba.

Shirin dai zai tilasta wa kasashen na Turai su rarraba 'yan gudun hijrar a tsakanin su.

Sai dai alamu na nuna cewa kai ya rabu a tsakanin kasashen.

Luxemberg da Jamus sun ce akasarin kasashen sun amince da shirin, amma za a yi cikakken bayani kan yadda za a aiwatar da shi a wani taron da za a kara yi a watan Oktoba.

Wasu kasashen dai na cewa aiwatar da shirin dibar kason 'yan hijrar ka iya tunzura mutane su kara kwarara zuwan turan, al'amarin da yake cike da hadari.

Tuni kuma wasu kasashe da suka hada da Jamus da Austria suka fara tsaurara matakan rufe kan iyakokinsu.

Gwamnatin Jamus ta bukaci Tarayyar Turai ta hana kudaden tallafin da za a bai wa duk kasar da ta ki karbar 'yan gudun hijirar.

Sai dai gwamnatin Hungary ta kaddamar da doka mai tsauri wacce za ta takaita kwararar 'yangudun hijira cikin ta.