Amfani da Komfuta na dakushe kwazon dalibai?

Image caption Amfani da kwamfiyutoci a makarantu na dakushe hazakar dalibai

Wani bincike na kasa da kasa ya gano cewa kashe kudade ta hanyar samar da kwamfiyutoci a makarantu ba ya kara kwazon dalibai.

Binciken wanda kungiyar hadin kan kasashe don bunkasar tattalin arziki ta Economic Co-operation and Development ta wallafa, ya gano cewa kasashen da suka fi amfani da fasahar zamanin ta kwamfiyuta za su fi samun nakasu ta fannin kwazon dalibai.

Shugaba mai kula da bangaren ilimi na kungiyar, Andreas Schleicher, ya ce yin amfani da kwamfiyuta a makarantu wanda yake sanya makarantun su kashe biliyoyin daloli a kowace shekara yana da matukar karya gwiwa.

Ya ce sakamakon ya nuna cewa ko da a matakin daidai kuwa, daliban da suke amfani da kwamfiyuta a makaranta suna da karancin yin katabus a azuzuwan nasu sabanin wadanda ba sa amfani da kwamfiyutar.

'Malamai ba sa maida hankali'

Wani kwararre a kan halayyar dalibai Tom Bennett, ya ce kwamfiyutoci sun rufe wa Malamai ido ta yadda har ba sa mayar da hankali wajen koyar da daliban.

Masu binciken dai sun gano cewa tsarin ilimin kasashen yankin Asiya wanda ke kan gaba a duniya ba kasafai yake amfani da na'urorin ba a makarantu.

Mista Schleicher ya ce "Daliban da ba su cika amfani da a kwamfiyutoci sosai ba sun fi katabus a harkar karatu fiye da daliban da ko yaushe suna makale da kwamfiyuta."

Masu sharhi a kan fasaha sun kimanta yawan kudin da ake kashewa duk shekara wajen sayen kwamfiyutoci a makarantu da cewa ya kai pam biliyan 17.5. A Biritaniya kuwa ana kashe pam miliyan 900 wajen sayen kwamfiyutoci na makarantu.

Kungiyar masu samar da kayan karatu na Biritaniya BESA, ta ce ana ware wa bangaren fasahar sadarwa ta zamani na makarantu pam miliyan 619 a kasafin kudin kasar.

Mista Schleicher ya yi gargadi cewa yawan amfani da kwamfiyuta a makarantu zai sa yara su sami dabarar wanko amsar ayyukan da ake basu su yi a gida a intanet, ba tare da sun yi kokarin samun amsar da kansu ba.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mista Schleicher ya yi gargadi cewa dalibai na iya satar amsa a kwamfiyuta

Binciken ya kuma nuna cewa babu wata kasa da aka samu wadda dalibai ke yawan amfani da kwamfiyuta sannan kuma a samu dalibansu da matukar kwazo da hazaka.

An gano cewa kasashe bakwai sune wadanda suka fi amfani da intanet a makarantu, Australia da Denmark da Greece da Sweden da Spain da Norway da kuma New Zealand.

'Dabi'ar son yin karatu ta ragu'

Dabi'ar son yiin karatu ta ragu a makarantun uku daga cikin wadannan kasashe wato Australia da New Zealand da Sweden, yayin da kuma ba a samun wani ci gaba a sakamakon dalibai a makarantun Spain da Norway da Denmark.

Kasashe da biranen da ba a faye amfani da kwamfiyutoci a makarantunsu ba kuwa sun hada da Korea ta Kudu da birnin Shanghai na China da Hong Kong da kuma Japan, kuma sune wadanda suka fi nuna kwazo a gwajin da aka yi na duniya.

Amma fa Mista Schleicher ya ce ba daidai ba ne sakamakon wannan bincike ya zama uzuri wajen kin amfani da kwamfiyutoci, sai dai a yi kokari a nemo hanyar warware wannan matsala cikin sauki.

'Yawan kwamfiyutoci a makarantun Biritaniya'

Akwai kwamfiyutar teburi kimanin miliyan daya da dubu 300.

Kwamfiutar tafi a gidanka kuwa ta kai dubu 840.

An kuma gano cewa ana amfani da kwamfiyutar ipad dubu 730, ana kuma zato yawan zai haura zuwa dubu 939 nan da bara.

Daga cikin dukkan wadannan, kashi 22 cikin 100 ne kawai ba a cika amfani da su ba.