Za a yi zanga-zanga a Congo

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaban Jamhuriyar Congo, Joseph Kabila

Wasu jam'iyyun adawa a jamhuriyar Dimukradiyar Congo za su yi zanga-zanga a babban birnin kasar, Kinshasa, a ranar Talata.

Za dai a yi zanga-zangar ne domin nuna adawa da duk wani yunkuri na dage zaben shugaban kasar da za a yi a watan Nuwamban 2016.

A makon jiya ne, babbar kotun kasar ta bukaci a sake nazarin jadawalin zaben, wani abu da 'yan adawa suka ce dabara ce ta bai wa shugaba Joseph Kabila damar ci gaba da mulki bayan cikar wa'adinsa.

Zanga-zanga da dama a kan nuna adawa da jinkirta zaben da aka gudanar sun rikide zuwa tashin hankali a watan Janairu, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 36.