BH: Faransa ta yi alkawarin taimaka wa Nigeria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Faransa ya yi alkawarin taimakawa Najeriya

Shugaban Faransa Francois Hollande, ya yi alkawarin taimaka wa Najeriya da kayan tattara bayanan sirri da na aikin soji domin yakar kungiyar Boko Haram.

Mista Hollande, ya yi wannan sanarwa ce yayin da yake tattaunawa da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, wanda yake ziyarar kwanaki uku a Faransa.

Ya ce gwamnatinsa ta damu da karuwar rashin tsaro a Najeriya da makwabtanta.

A bara ne shugaban na Faransa ya jagoranci wani taro da aka yi a birnin Paris a kan lamarin rikice-rikicen kungiyar Boko Haram.