Saudi ta dakatar da kamfanin Bin Laden

Kugiyar da ta fada kan masallcin Makkah a Saudiyya. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kugiyar da ta fada kan masallcin Makkah a Saudiyya.

Jami'an Saudiya sun dauki mataki a kan kamfani gine gine na Bin Ladin bayan da daya daga cikin na'urorin daukar kayan gininsa ya fada a babban Masallacin Makkah.

Mahajjata fiye da dari ne dai suka mutu a hadarin ranar juma'a, har da 'yan Nijeriya shidda, yayinda wasu sama da dari biuyu suka jikkata.

An haramta wa kamfanin -- karbar wata sabuwar kwangila har sai an kammala bincike.

Wakilin BBC ya ce, babbar tozartawa ce ga kamfanin, wanda mahaifin marigayi shugaban kungiyar AlQaida, Osama Bin Laden ya kafa, kuma ya bunkasa har ya zama daya daga cikin kamfanonin Saudiya mafiya girma.

Za a yi nazari ayyukan da yake yi a halin yanzu, kuma ba za a bar manyan jami'ansa su bar kasar ba.