Koriya na shirin kai wa Amurka hari

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu hotunan tauraron dan adam sun nuna yadda Koriya ke ci gaba da ayyukan kera makaman nukiliyar.

Kasar Koriya ta arewa ta ce ta kara kaimi a aikin da take yi na kera makaman nukiliya a babbar tashar nukiliyarta da ke Yongbyon.

Kasar ta ce tana so ne ta inganta yadda take kera makaman nukiliyarta, kuma a shirye take ta kai wa Amurka hari da su a kowanne lokaci.

Wasu hotunan tauraron dan adam da aka fitar a makon jiya sun nuna yadda ake ci gaba da ayyukan a yankunan da ake kera makaman nukiliyar na Koriya ta arewa.

Wannan sanarwa na zuwa ne kwana guda bayan kasar ta ce tana shirin kaddamar da wadansu tararin dan adam, lamarin da ke nuna cewa za ta iya kai harin roket na dogon-zango.

Masu sharhi na ganin Koriya ta arewa ta fitar da wadannan sanarwa guda biyu ne domin ta nuna wa duniya cewa tana da karfin soji.