An yi artabu tsakanin Yahudawa da Palasdinawa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kasar Jordan ta yi gargadin cewar dole ne Isra'ila ta dawo da zaman lafiya a yankin da masallacin yake ko kuma dangantaka tsakaninsu ta yi tsami.

A rana ta uku jere, 'yan sandan Isra'ila sun yi artabu da Palasdinawa masu zanga-zanga a zagayen masallacin birnin Qudus.

Masallacin -- da ke a bangaren gabashin birnin wanda Isra'ila ta mamaye -- yana da tsarki ga dukkanin Yahudawa da musulmi, kuma ya kan kuma kasance wani wurin zaman dar dar.

Majalisar Dinkin Duniya da Amurka sun bukaci a kwantar da hankali.

Kasar Jordan mai makwabtaka kuma ta yi gargadin cewar dole ne Isra'ila ta dawo da zaman lafiya a yankin da masallacin yake ko kuma dangantaka tsakaninsu ta yi tsami.