Buhari ba shi da alkibla — PDP

Image caption PDP ta ce Buhari ya jefa Najeriya cikin mawuyacin hali.

Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya, PDP, ta ce shugaban kasar Muhammadu Buhari ba shi da alkibla tun da ya hau karagar mulki.

Kakakin jam'iyyar, Cif Olisa Metuh, ya shaida wa BBC cewa hakan ne ya sa tattalin arzikin kasar ke ci gaba da tabarbarewa.

A cewar sa, rashin sanya ginshikin da zai nuna alkiblar da tattalin arzikin kasar ya dosa ya sa kasar ta fada mawuyacin hali.

Sai dai Sakataren jam'iyyar APC mai mulki, Mai Mala Bunu ya musanta zargin da PDP ta yi, yana mai cewa PDPn ce ta durkusar da tattalin arzikin Najeriya.

Ya kara da cewa gwamnatin Muhammadu Buhari tana so ne ta gyara barnar da PDP ta kwashe shekara-da-shekaru tana yi wa kasar.

Mala Bunu ya ce 'yan jam'iyyar ta PDP suna yin korafi ne kawai saboda zafin kayen da suka sha a zaben da aka yi a watannin Maris da Aprilu na wannan shekarar.