Wata makidiya a Kenya ta lashe Gasar fina finai

Image caption Makena ta bayyana mataukar jin dadin ta saboda lashe gasar.

Wata shahararriyar makidiya 'yar kasar Kenya, Pierra Makena ta lashe gasar jarumar fina finai a rawar da ta taka a wani fim na na Najeriya mai suna ''When Love Comes Around''.

Makena ta lashe gasar ne a wajen bikin bayar da kyautar fina finai na Nollywood & African Film Critics' Awards, wanda aka fi sani da the African Oscars.

Mutane da dama sun yi mamaki da aka ayyana Makena a matsayin wacce ta lashe gasar saboda ta fi yin fice ne a fanni kida.

A wani sako da ta wallafa a shafinta na Instagram, Makena ta bayyana mataukar jin dadin ta saboda lashe gasar.

Makena ta doke Eku Edewor, Sonia Ibrahim, Taiwo Ajayi Lycett Vivica, wadanda su ma suka yi takarar cin gasar.