Booker: An tantance ɗan Nigeria

Hakkin mallakar hoto booker prize

Marubuci ɗan Nigeria Chigozie Obioma ya shiga sahun marubutan da aka tantance domin lashe lambar yabo ta marubuta da harshen Turanci wato Booker Prize.

Ɗan shekaru 28, Obioma shi ne mafi ƙuruciya cikin marubutan da aka tantance da littafinsa na farko da ya rubuta mai suna 'Fishermen'.

Sauran marubutan da aka tantance sun haɗa da Marlon James wanda shi ne ɗan Jamaica na farko da ya shiga wannan mataki.

Kowanne daga cikin marubutan da aka tantance zai samu kyautar £2,500, wanda ya lashe kyautar zai samu £50,000.

A baya dai dan Najeriya Ben Okri ya taɓa lashe wannan kyauta da littafinsa mai suna 'The Famished Road'.