Mun soma tattaunawa da Boko Haram — Buhari

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A shekarar 2014 ne kungiyar ta Boko Haram ta sace 'yan makarantar Chibok fiye da 200.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa tana tattaunawa da kungiyar Boko Haram domin ta saki 'yan matan Chibok.

Shugaban ya bayyana haka ne a birnin Paris a lokacin da yake ganawa da 'yan Najeriya mazauna Faransa.

Shugaba Buhari ya ce,"Batun 'yan matan Chibok yana cikin zukatanmu, kuma saboda yadda batun ya ja hankulan kasashen duniya shi ya sa gwamnatinmu ke tattaunawa da shugabannin kungiyar ta Boko Haram".

Shugaban na Najeriya ya kara da cewa matakin farko da suka dauka shi ne na gano hakikanin shugabannin kungiyar, yana mai cewa sun yi hakan ne domin gujewa tattaunawa da shugabannin bogi.

A cewar sa, kungiyar ta bukaci jami'an tsaron kasar su saki wani babban jami'inta da ya kware wajen kera abubuwan fashewa, yana mai cewa gwamnatinsa ba za ta taba amincewa da wannan bukata ba.

A watan Aprilun shekarar 2014 ne dai 'yan kungiyar ta Boko Haram suka sace 'yan makarantar Chibok fiye da 200.

Shugaban kasar na wancan lokacin, Goodluck Jonathan, ya sha suka bisa rashin daukar matakan gaggawa domin ceto 'yan matan.