Kwalara: Mutane 9 sun mutu a sansanin 'yan gudun hijira

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dubban mutane ne ke samun mafaka a sansanonin 'yan gudun hijira.

Hukumomi a Najeriya sun ce mutane tara ne suka mutu cikin mutane 96 da suka kamu da cutar amai da gudawa a sansanin 'yan gudun hijira na Sandikyarini da ke birnin Maiduguri a jihar Borno.

Babban jami'in hukumar bayar da agajin gaggawa a yankin arewa maso gabas, Muhammad Kanar, ya shaida wa BBC cewa mutane shida ne kawai suke jinya.

A cewar sa, suna kokarin shawo kan lamarin.

Mutane sama da 5000 dai ke neman mafaka sansanin sakamakon hare-haren da kungiyar Boko Haram ta kai musu.