Zan iya karbar mukami — Jega

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Farfesa, Attahiru Jega, tsohon shugaban hukumar INEC

Tsohon shugaban hukumar zaben Najeriya, Farfesa Attahiru Jega ya ce a shirye yake ya amsa kiran sake yi wa kasarsa aiki idan dai aka bukace shi da yin hakan.

Gabanin barin mukaminsa a watan Yuni, Farfesa Jega ya kawar da yiwuwar ci gaba da shugabantar hukumar zaben.

Sai dai Farfesa Jega ya shaida wa BBC cewa yanzu zai iya karbar wani mukami domin ci gaban kasarsa.

Farfesa Jega dai ya samu yabo a idon duniya a kan yadda ya jagoranci babban zaben kasar na shekara ta 2015, wanda ake gani shi ne mafi sahihanci a dimokradiyyar kasar.

A yanzu haka dai Farfesa Jega ya koma Jami'ar Bayero da ke Kano inda yake ci gaba da koyarwa.