Miliyoyin 'yan Afrika sun kubuta daga maleriya

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Cutar zazzabin cizon Sauro

Wani sabon nazari da aka yi ya nuna cewar gangamin yaki da zazzabin cizon sauro a Afrika ya kare mutane miliyan 700 daga kamuwa da nau'in cutar mafi muni tun farkon karnin nan.

Binciken da wata tawagar Jami'ar Oxford ta gudanar a karon farko, ya tantance tasirin matakan da aka dauka a ko'ina cikin nahiyar a inda galibi ake mutuwa sakamakon cutar zazzabin cizon sauron.

Binciken ya gano cewar mutanen da ke kamuwa sun ragu ya zuwa rabi.

Sai dai rahoton ya ce har yanzu ba a bayar da lasisi ga allurar riga kafin zazzabin cizon sauro ba, sannan akwai karuwar damuwa game da bijirewa ainihin maganin da ake amfani da shi wajen magance cutar.

Binciken ya ce kasashe 13 da suke da wadanda ke da cutar ta Maleriya a shekarar 2000, a shekarar da ta gabata ba a samu wanda ya kamu da cutar ba, yayin da a wasu kasashe shida kuma ana samun wadanda suka kamu da cutar mutum 10, ko ma kasa da haka.

Darakta Janar ta hukumar lafiya ta duniya, Dr Margaret Chan, ta ce batun yaki da cutar zazzabin cizon sauro a duniya ya samu babbar nasara a cikin shekaru 15.

Ta ce hakan ya nuna cewa matakan da ake dauka na bisa ka'ida.

Sai dai duk da nasarar yaki da cutar da ake samu, har yanzu yara na mutuwa sakamakon kamuwa da cutar.

A saboda haka masana suka bayar da shawarar rubanya kokarin da ake yi wajen kawar da ita kwata-kwata a duniya baki daya.