'Yan bindiga sun kashe mutane 20 a Mangu

Image caption Daya daga wuraren da aka kai hari a Najeriya

A Nijeriya, mutane akalla ashirin sun rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka jikkata a wani hari da 'yan bindiga suka kai garin Kadunung a karamar hukumar Mangu ta jihar Plateau.

Maharan sun dirar wa garin da mugan makamai inda suka rika bude wuta ba kakkautawa ranar Talata tare da kona gidaje.

Rahotanni sun ce tun a ranar Litinin aka fara samun barazanar kai hari a yankin.

Mazauna garin da suka tsere daji sakamakon harin sun ce suna zargin wasu 'yan kabilar Berom da kaddamar da harin, sai dai wasu shugabannin kungiyar kabilar Berom din basu ce komai ba.

an tura jami'an tsaro yankin domin maido da doka da oda.