'Ya kamata a daina yin 'yar tsana don jima'i'

Hakkin mallakar hoto
Image caption Wasu dai na amfani da 'yar tsana wajen jima'i

Wata masaniyar halayyar butum-butumi a Jami'ar Leicester, Dr Kathleen Richardson, ta soki yadda wasu suke amfani da 'yar tsana domin biyan bukatarsu ta jima'i.

Ta ce fasahar kirkirar butum-butumin domin jima'i ba ta zama dole ba.

Yanzu haka dai butum-butumin ya cika kasuwanni.

Sai dai kuma Dr. Richardson tana kokarin wayar da kawunan masu amfani da 'yar tsana domin yin jima'i da su guji hakan.

Ta ce, "kirkirar 'yar tsana domin jima'i yana karuwa a tsakanin masu fasahar butum-butumi".

Hakkin mallakar hoto THINKSTOCK
Image caption Dr. Richardson tana son a daina wannan al'ada

Dr. Richardson ta ce ta yi imanin cewa masu yin 'yar tsanar suna kara wa mutane irin tunanin da suke da shi na cewa mata an yi su ne saboda jima'i.