'Sri Lanka ta aikata laifukan yaki'

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Sun aikata laifukan ne a lokacin yakin basasa.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akwai alamu masu karfi da ke nuna cewa gwamnatin Sri Lanka da 'yan tawayen Tamil Tigers sun aikata laifukan yaki da cin zarafin al'umma.

Majalisar ta ce bangarorin biyu sun yi hakan ne a lokacin yakin basasar kasar da aka kawo karshensa shekaru shida da suka wuce.

A wani muhimmin rahoto da ofishin hukumar kare hakkin bil Adama na Majalisar ya fitar, shugaban hukumar, Zeid Ra'ad AL Hussein, ya ce wajibi ne a kafa kotun musamman ta hadin gwiwa wadda za ta kunshi alkalai na kasa-da-kasa da lauyoyi domin binciken ta'asar.

A martanin ta, gwamnatin kasar ta yi alkawarin tabbatar da adalci, kodayake ba ta ce komai ba game da kafa kotun musamman ta hadin gwiwar.