Kare ya sauya akalar jirgin sama

Image caption Mai karen German Kontorovich ya godewa matukin jirgin.

Wani jirgin saman Canada ya juya akalarsa bayan da matukin ya gane cewa wata na'urar da ke dumama bangaren da ake zuba kaya na jirgin ta daina aiki, wanda lalacewar na'urar ka iya jefa rayuwar wani kare cikin hadari.

Karen mai suna Simba mai kimanin shekaru bakwai, yana bangaren zuba kaya na jirgin ne, wanda in wajen ba dumi sanyi zai iya hallaka shi yayin da aka lula sama sosai.

Jirgin ya tashi ne a ranar Lahadi daga birnin Tel Aviv na Isra'ila zuwa birnin Toronto na Canada, sai matukin ya juya akalarsa zuwa birnin Frankfurt na Jamus.

Hakan ya janyo an bata wa fasinjoji kusan 200 da ke cikin jirgin lokaci na fiye da sa'a daya.

Mai magana da yawun kamfanin jirgin Peter Fitzpatrick, ya ce "A karshe dai an cimma abin da ake so, musamman ma da yake fasinjojin sun fahimci cewa an ceto karen ne daga hallaka."

Mai karen German Kontorovich, ya ce "Na gode wa matukin nan kwarai da ya ceto karena, don kamar da yake a wajena."