Sojoji sun yi juyin mulki a Burkina Faso

Image caption An nada daya daga cikin dakaru, Janar Gilbert Diendere, a matsayin shugaban gwamnatin rikon kwaryar.

Sojoji a Burkina Faso sun ce sun kifar da gwamnatin rikon kwaryar kasar karkashin jagorancin shugaba Michel Kafando.

A jawabi ta gidan talabijin na kasar, dakarun fadar shugaban kasar sun ce sun rushe abin da suka kira "fandararriyar gwamnatin rikon kwarya".

An nada daya daga cikin dakarun, Janar Gilbert Diendere, a matsayin shugaban gwamnatin rikon kwaryar.

Sojin sun rufe dukkanin iyakokin kasar, sannan suka sanya dokar hana fita.

Shugaban majalisar dokokin kasar ya yi kira ga rundunar soji da ta karbe mulki domin ta tsayar da abin da ya kira aikin "wasu tsirarun sojoji".

Dakarun fadar shugaban kasar sun yi ta harbe-harbe a Ouagadougou a matsayin gargadi ga mutanen da suka taru domin yin zanga-zanga.

A bara ne dai aka hambarar da Shugaba Blaise Compaore -- wanda ya shafe shekaru 27 yana mulki -- a yayin wata zanga-zangar kin-jinin mulkinsa.

An dai shirya gudanar da zabukan ne a ranar 11ga watan Oktoba.