Zanga-zanga ta barke a Burkina Faso

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan kasar da dama sun yi zanga-zangar kin-jinin juyin mulkin.

Zanga-zangar da ta barke bayan sojin da ke fadar shugaban kasa a Burkina Faso sun yi juyin mulki ta yi sanadiyar mutuwar a kalla mutane 10 a Ouagadougou, babban birnin kasar.

A jawabi na gidan talabijin din kasar da dakarun suka yi, sun nada wani na hannun daman tsohon shugaba Blise Compaore, Janar Gilbert Diendere, a matsayin sabon shugaban kasar.

Shugaban Faransa, Francois Hollande, ya yi Allah wadai da juyin mulkin da aka yi a kasar da Faransar ta raina.

Wata kungiyar fararen hula ta ce dakarun fadar shugaban kasar ne suka harbe mutanen har lahira.

Sai dai ba bu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da ikirarin da kungiyoyin fararen hula suka yi na yawan mutanen da aka kashe din.

An kifar da "fandararriyar gwamnati"

A safiyar Alhamis ne dai sojojin suka ce sun kifar da gwamnatin rikon kwaryar kasar karkashin jagorancin shugaba Michel Kafando.

Dakarun sun ce sun rushe abin da suka kira "fandararriyar gwamnatin rikon kwarya".

Sojin sun rufe dukkanin iyakokin kasar, sannan suka sanya dokar hana fita.

A bara ne dai aka hambarar da Shugaba Blaise Compaore -- wanda ya shafe shekaru 27 yana mulki -- a yayin wata zanga-zangar kin-jinin mulkinsa.

An dai shirya gudanar da zabukan ne a ranar 11ga watan Oktoba.