Kotu ta dakatar da shari'ar Bukola Saraki

Hakkin mallakar hoto bukola
Image caption Shugaban majalisar dattijai Dr. Bukola Saraki

Wata kotu a Abuja ta dakatar da yunkurin hukumar kula da da'ar ma'aikata ta Najeriya na gurfanar da shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki a gaban kotun da'ar ma'aikata bisa zargin karya wajen bayyana kadarorinsa.

Wannan ya zo ne bayan da lauyoyin Saraki suka kalubalanci yunkurin hukumar a gaban kotun tarayya a bisa tuhume-tuhume guda 13 da suka shafi zargin karya wajen bayyana kadarorinsa.

Tuni dai shugaban majalisar dattawan, Bukola Saraki ya musanta zargin da hukumar kula da da'ar ma'aikata ke yi masa.

Mai shari'a Justice Ahmed Mohammed ne ya yanke hukuncin dakatarda da sauraren shari'ar da aka shirya yi a safiyar yau.

Ya kuma nemi shugaban kotun hukumar kula da da'ar ma'aikata da ya bayyana a gaban babbar kotun a ranar 21 ga wannan watan Satumba domin ya gamsar da ita a kan dalilan da shugaban majalisar dattawan zai gurfana a gaban shari'a domin ya amsa zargin da ake yi masa.

Kotun ta kuma nemi mataimakin darakta a ofishin babban mai shari'a na kasar Mista M.S Hassan, wanda ya sa hannu a kan takardar tuhumar da ake yi wa Sanata Bukola Sarakin, da shi ma ya bayyana a gabanta.

Kotun dai ta bayar da umarnin ne bayan da ta saurari bukatar da Dr. Sarakin ya shigar ta hannun lauyansa Mista Mahmoud Magaji.