Saudiyya za ta ba Nigeria diyya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sarki Salman ya bukaci a biya diyya Riyal miliyan daya ga iyalan mutanen da suka rasu.

Hukumar aikin Hajji ta Najeriya ta ce tana ci gaba da daukar matakan tabbatar da cewa 'yan kasar wadanda hadarin da ya auku a Harami ya shafa sun sami diyyar da Sarki Salman ya bayar da umarnin a biya su.

Wadanda za su samu diyyar dai sun hada da dangin wadanda suka rasu da kuma wadanda suka samu raunuka.

Za a bai wa dangin wadanda suka rasu diyyar Riyal miliyan guda na Saudiyya, yayin da wadanda hatsarin ya nakasa su za su samu Riyal miliyan guda.

Kazalika za a bai wa wadanda suka samu raunuka Riyal dubu dari biyar.

Hatsarin dai ya yi sanadiyar rasuwar mutane 107, cikin su har da 'yan Najeriya guda shida.