AU ta dakatar da Burkina Faso

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugabar Tarayyar Afrika Nkosazana Dlamini Zuma.

Kungiyar tarayyyar Afrika AU, ta dakatar da kasar Burkina Faso daga dukkan al'amuran da suka shafeta nan take.

Kungiyar ta dauki matakin bayan ta kammala wani taro a kan rikicin da ke faruwa a Burkina Faso.

AU ta kuma yi Alla-wa-dai da sace shugaban gwamnatin rikon kwarya, da Firai minista, da kuma wasu ministocin gwamnatin kasar da sojojin juyin mulkin suka yi, tana mai cewa hakan "aikin ta'addanci ne."

Kazalika, kungiyar ta ce, za ta kakabawa wa wadanda suka yi juyin mulkin takunkumi, da zummar ganin sun saki shugabannin gwamnatin rikon kwaryar da suka tsare nan take ba.

A safiyar ranar Alhamis ne sojojin kasar suka ce sun kifar da gwamnatin rikon kwaryar kasar karkashin jagorancin shugaba Michel Kafando.