Burkina Faso: An saki Michel Kafando

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An kama Mr Kafando ne bayan taron majalisar zartarwar kasar.

Sojojin da suka yi juyin mulki a Burkina Faso sun ce sun saki shugaban gwamnatin rikon-kwarya na kasar Michel Kafando, kuma yana cikin koshin lafiya.

Sai dai sun ce sun yi daurin-talala ga Firai Ministan kasar Isaac Zida.

Kazalika, an saki ministoci biyu wadanda su ma aka kama su tare da shugabannin biyu.

Sojojin sun kuma amince a tattauna, a daidai lokacin da shugabannin kasashen Afirka guda biyu ke kan hanyarsu ta zuwa kasar domin nemo bakin-zare a kan rikicin siyasar kasar.

Dakarun tsaron fadar shugaban kasar ne suka kama Mr Kafando da Firai Ministan kasar ranar Laraba a lokacin da ake gudanar da taron majalisar zartarwar kasar.

A kalla mutane uku ne suka mutu a yayin wata zanga-zanga bayan sojin sun ayyana wani na hannun-daman tsohon shugaban kasar, Blaise Compaore, a matsayin shugaban wucin-gadi.

Kasashen Amurka da Faransa da kungiyar Tarayyar Afirka sun yi Alla-wadai da juyin mulkin.