Burkina Faso: Za a saki Michel Kafando

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An kama Mr Kafando ne bayan taron majalisar zartarwar kasar.

Sojojin da suka yi juyin mulki a Burkina Faso sun ce za su saki shugaban kasar na wucin-gadi wanda aka tsare, Michel Kafando.

Sun bayar da wannan tabbaci ne a wata sanarwa da aka karanta a gidan talabijin na kasar.

Sojojin sun kuma amince a tattauna, a daidai lokacin da shugabannin kasashen Afirka guda biyu ke kan hanyarsu ta zuwa kasar domin nemo bakin-zare a kan rikicin siyasar kasar.

Dakarun tsaron fadar shugaban kasar ne suka kama Mr Kafando da Firai Ministan kasar ranar Laraba a lokacin da ake gudanar da taron majalisar zartarwar kasar.

A kalla mutane uku ne suka mutu a yayin wata zanga-zanga bayan sojin sun ayyana wani na hannun-daman tsohon shugaban kasar, Blaise Compaore, a matsayin shugaban wucin-gadi.

Kasashen Amurka da Faransa da kungiyar Tarayyar Afirka sun yi Alla-wadai da juyin mulkin.