'Za a yi zabe a Burkina Faso'

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaban juyin mulkin Burkina Faso Janar Gilbert Diendere

Sojojin da suka yi juyin mulki a Burkina Faso sun yi alkawarin mika mulki ga farar hula nan ba da dadewa ba.

Janar Gilbert Diendere shi ya bayana hakan a hirarsa da BBC.

Janar din dai bai fadi ranar da za a gudanar da zaben a kasar ba.

Ya kara da cewa, "mika mulkin ba zai yiwu ba har sai an cimma yarjejeniyar da za ta daidait kasar da kuma bayar da damar ci gaba da shirye-shiryen yin zabe cikakke".

Shugaba Macky Sal na Senegal da Bonu Yayi na Benin, na yin ziyara a Burkina Faso, inda suke ci gaba da tattaunawa da shugabannin siyasa da na kungiyoyin farar hula da masu fafutuka a Wagadugu, babban birnin kasar.