Dan jaridar Ghana da ya fasa kwai ya shiga Kotu

Image caption Anas Aremeyaw Anas yana yawan badda kamaninsa

Dan jaridar nan na Ghana mai badda kama , wanda ya ce ya dauki bidiyon alkalan kasar suna karbar hanci, kamar yadda yayi zargi, ya bayyana a ofishin Cif Joji amma fuskarsa a rufe.

Anas Aremeyaw Anas ya je ofishin ne domin ya bayar da shaida game da bidiyon nasa a gaban kwamitin.

A lokacin ne aka shirya wasu lauyoyi za su yi masa tambayoyi a madadin alkalan.

Amma kwamitin ya jingine zamansa saboda ya ce an samo wani umarnin kotu da ya ce su fayyace abubuwa kafin su ci gaba.

Ko da yaushe Mista Anas ya kan sanya gemu a fuskarsa saboda ya bad da kama kuma mutanen da suka fi kusa da shi ne kawai suke ganin ainihin fuskarsa.