An gama jigilar maniyyata a Nigeria

Image caption Aikin Hajj

Hukumar alhazan Najeriya ta ce ta kammala jigilar maniyyatan aikin hajjin bana zuwa kasar Saudiyya.

Shugaban hukumar alhazan Alhaji Abdullahi Mukhtar Mohammed wanda ya tabbatar wa da BBC hakan inda ya ce an kwashe maniyyatan Najeriya kimanin dubu 66.

Ya kara da cewa an kwashe maniyyatan ne a jigila 160, kuma jiragen karshe sun tashi ne daga filayen jirgin sama na Kano da Fatakwal da Abuja.

Hukumar ta ce ta kammala jigilar ne kwana guda kafin rufe filin jirgin sama na Sarki Abdul-aziz da ke Jidda.