An kashe sojojin Pakistan 17

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hari a Pakistan

Rundunar sojin Pakistan ta ce an kashe jami'anta goma sha bakwai a wani hari da 'yan bindiga suka kai a sansanin sojin sama da ke birnin Peshawar.

Rundunar ta ce an kashe sojoji 16 ne a lokacin da suke yin sallah a wani masallaci da ke cikin wani gida.

Ta kara da cewa an kashe daya sojan ne -- mai mukamin kyaftin -- a lokacin da yake jagorantar sojoji domin dakile harin.

Fiye da mutane 20 ne suka jikkata sakamakon harin.

Kakakin rundunar sojin, Asim Bajwa, ya ce an kashe 'yan bindiga goma sha uku, yana mai cewa ana ci gaba da gumurzu.

Ya kara da cewa 'yan bindigar sun kai harin ne sanye da kakin soji.

Kungiyar Taliban ta ce ita ta kai harin, kuma mambanta daya ne kawai ya mutu.