Burkina Faso: Tashin hankali ya ɓarke

Mummunan yamutsi ya ɓarke a wani Otel a Wagadugu babban birnin Burkina Faso inda ake tattaunawa dangane da juyin mulkin da aka yi a ƙasar cikin makon jiya.

Masu zanga-zanga suna ta ɗaga kwalaye, da kuma rera waƙoƙi na nuna goyon baya ga dakarun dake tsaron fadar shugaban kasar da suka tumɓuke gwamnatin riƙon ƙwarya da Michel Kafando ke jagoranta.

Dama dai an shirya masu shiga tsakani na ƙungiyar ƙasashen yammacin Afirka ECOWAS za su yi jawabinsu na ƙarshe akan ƙoƙarin warware juyin mulkin da ƙarfe goma na safe.

Amma saboda zanga-zangar hakan bata yiwu ba, sai ma da aka nemi daukin jami'an tsaro.

Jiya ne dai masu shuga tsakanin dake tattaunawa da wadanda suka yi juyin mulkin suka bayyana cewa, suna daf da maida mulki ga gwamnatin farar hula.

Tun daga ranar da aka yi juyin mulkin dai an kashe akalla mutane goma a karawa tsakanin masu zanga-zanga da jami'an tsaro.