Ethiopia ta ƙaddamar da layin dogo

Hakkin mallakar hoto s

An gudanar da bukukuwa a Addis Ababa babban birnin Ethiopia yayin kaddamar da tsarin sufurin jiragen kasa da zai saukaka zirga-zirga.

Hukumomi sun ce, layin dogon na Addis Ababa zai yi aikin awa 16 kowacce rana.

Sabon tsarin sufurin zai kuma samar da tsarin sufuri mai nagarta ga mazauna birnin.

Wannan dai shi ne tsarin sufurin jirgin kasa mai aiki da lantarki na farko yankin Afirka dake kudu da Sahara.

Aikin baki ya lashe dalar Amurka $470.

Yawancin biranen Afirka dai sun dogara ne da motoci domin sufuri, lamarin da kan haifar da cinkoso dake shafar dukkan bangarorin rayuwa.

A